Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 9:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Hikima ta gina gidanta, ta yi masa ginshiƙai bakwai.

2. Ta sa an yanka dabba don biki, ta gauraya ruwan inabi da kayan yaji, ta shirya tebur.

3. Ta aiki barorinta 'yan mata su je su hau wuri mafi tsayi a birni su yi kira.

4. “Ku shigo, ku jahilai!” Ga dolo kuwa ta ce,

5. “Zo ka ci abincina ka sha ruwan inabin da na gauraya.

6. Ka rabu da ƙungiyar jahilai, ka rayu, ka bi hanyar ilimi.”

7. Idan ka kwaɓi mai fāriya, za ka gamu da cin mutunci, idan ka tsauta wa mugu, kai ne za ka cutu.

8. Faufau kada ka kuskura ka kwaɓi mai fāriya, zai ƙi ka saboda wannan, amma idan ka kwaɓi mai hikima zai girmama ka.

9. Dukan abin da ka faɗa wa mutum mai hikima, zai ƙara masa hikima. Dukan abin da ka faɗa wa adali zai ƙara masa ilimi.

10. Domin ka zama mai hikima dole ka fara da tsoron Ubangiji. Idan ka san Mai Tsarki, ka sami ganewa.

11. Hikima za ta ƙara shekarunka.

12. Kai ne da riba in ka sami hikima. Kai za ka sha hasara in ka ƙi ta.

Karanta cikakken babi K. Mag 9