Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 8:9-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ga mutum mai basira, dukan abu ne a sarari,Ga wanda aka sanar da shi sosai, abu ne a sawwaƙe.

10. Ka zaɓi koyarwata fiye da azurfa,Ka zaɓi ilimi fiye da zinariya tsantsa.

11. “Ni ce hikima, na fi lu'ulu'ai,Cikin dukan abin da kake so, ba kamata.

12. Ni ce hikima, ina da basira,Ina da ilimi da faɗar daidai.

13. Ƙin mugunta shi ne tsoron Ubangiji,Na ƙi girmankai, da fāriya, da mugayen hanyoyi,Da maganganu na ƙarya.

14. Nakan shirya abin da zan yi, in kuwa yi shi.Ina da fahimi, ina da ƙarfi.

15. Nakan taimaki sarakuna su yi mulki,Mahukunta kuma su tsara dokoki masu kyau.

16. Kowane mai mulki a duniya, da taimakona yake mulki,Ƙusoshin hukumomi da dattawan gari duka ɗaya.

17. Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata,Dukan wanda yake nemana kuma zai same ni.

18. Ina da dukiya da daraja da zan bayar,Da wadata da nasara kuma.

19. Abin da za ka samu daga gare niYa fi zinariya kyau, da azurfa tsantsa.

20. A kan hanyar adalci nake tafiya,Rankai a kan hanyoyin gaskiya.

21. Ina ba da dukiya ga waɗanda suke ƙaunata,Ina kuma cika gidajensu da wadata.

22. “Ni ce halittar farko da UbangijiYa fara halittawa daga cikin ayyukansa tuntuni.

23. Da farkon farawa ni aka fara halittawaKafin a yi duniya.

24. Ni aka fara yi kafin tekuna,A sa'ad da ba maɓuɓɓugan ruwa.

25. Ni aka fara yi kafin a yi duwatsu,Kafin a kafa tuddai a wurarensu,

26. Kafin Allah ya halicci duniya da filayenta,Ko ɗan ɓarɓashin ƙasa.

27. A can nake sa'ad da ya shata sararin sama,Da sa'ad da ya shimfiɗa al'arshi a hayin tekuna,

28. Da sa'ad da ya sa gizagizai a sararin sama,Ya buɗe maɓuɓɓugan teku,

29. Ya kuma umarci ruwan teku, kada ya zarce wurin da ya sa.Ina can sa'ad da ya kafa harsashin ginin duniya.

Karanta cikakken babi K. Mag 8