Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 8:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Kowane abu da na faɗa gaskiya ne,Ba wani abu da yake na laifi ko na ruɗawa.

9. Ga mutum mai basira, dukan abu ne a sarari,Ga wanda aka sanar da shi sosai, abu ne a sawwaƙe.

10. Ka zaɓi koyarwata fiye da azurfa,Ka zaɓi ilimi fiye da zinariya tsantsa.

11. “Ni ce hikima, na fi lu'ulu'ai,Cikin dukan abin da kake so, ba kamata.

12. Ni ce hikima, ina da basira,Ina da ilimi da faɗar daidai.

13. Ƙin mugunta shi ne tsoron Ubangiji,Na ƙi girmankai, da fāriya, da mugayen hanyoyi,Da maganganu na ƙarya.

14. Nakan shirya abin da zan yi, in kuwa yi shi.Ina da fahimi, ina da ƙarfi.

15. Nakan taimaki sarakuna su yi mulki,Mahukunta kuma su tsara dokoki masu kyau.

16. Kowane mai mulki a duniya, da taimakona yake mulki,Ƙusoshin hukumomi da dattawan gari duka ɗaya.

17. Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata,Dukan wanda yake nemana kuma zai same ni.

18. Ina da dukiya da daraja da zan bayar,Da wadata da nasara kuma.

Karanta cikakken babi K. Mag 8