Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 8:29-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Ya kuma umarci ruwan teku, kada ya zarce wurin da ya sa.Ina can sa'ad da ya kafa harsashin ginin duniya.

30. Ina kusa da shi kamar mai tsara fasalin gini,Ni ce abar murnarsa kowace rana,A ko yaushe ina farin ciki a gabansa.

31. Ina farin ciki da duniya,Ina murna da 'yan adam.

32. “Yanzu ku matasa, ku kasa kunne gare ni,Ku yi abin da na ce, za ku yi farin ciki.

33. Ku saurari abin da aka koya muku,Ku zama masu hikima, kada ku yi sakaci da ita.

34. Mutumin da ya kasa kunne gare ni, zai yi farin ciki haka nan,Wato yakan tsaya a ƙofata ko yaushe,Yana kuma jira a ƙofar shiga gidana.

35. Mutumin da ya same ni ya sami rai,Ubangiji zai ji daɗinsa.

36. Mutumin da bai same ni ba ya cuci kansa,Duk wanda yake ƙina mutuwa yake ƙauna.”

Karanta cikakken babi K. Mag 8