Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 7:2-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ka yi abin da na faɗa maka, za ka rayu. Ka natsu, ka bi koyarwata, ka tsare ta kamar ƙwayar idonka.

3. Kullayaumi ka riƙe koyarwata tare da kai, ka rubuta ta a zuciyarka.

4. Ka mai da hikima 'yar'uwarka, basira kuwa ta zama ƙawarka ta jikinka.

5. Za su nisanta ka da matan mutane, daga kuma mata masu maganganun alfasha.

6. Wata rana ina leƙawa ta tagar ɗakina,

7. sai na ga waɗansu samari masu yawa waɗanda ba su gogu da duniya ba, musamman sai na lura da wani dolo a cikinsu.

8. Yana tafe a kan titi kusa da kusurwar da take a zaune, yana wucewa kusa da gidanta,

9. da magariba cikin duhu.

10. Sai ta tarye shi, ta ci ado kamar karuwa, tana shirya yadda za ta yaudare shi.

11. (Ba ta jin tsoro, ba ta kuma jin kunya, ko yaushe tana ta gantali a tituna.

12. Takan tsaya tana jira a kowace kusurwa, wani lokaci a tituna, wani lokaci kuma a kasuwa.)

13. Ta rungumi saurayin, ta sumbace shi, ta dubi tsabar idonsa ta ce,

Karanta cikakken babi K. Mag 7