Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 7:18-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ka zo mu sha daɗin ƙauna, mu more dukan dare, mu yi farin ciki rungume da juna.

19. Mijina ba ya gida, ya yi tafiya mai nisa.

20. Ya tafi da kuɗi masu yawa, ba zai komo ba sai bayan mako biyu.”

21. Ta jarabce shi da kwarkwasarta, sai ya ba da kai ga daɗin bakinta.

22. Nan da nan ya bi ta kamar sā zuwa mayanka, kamar barewa tana tsalle zuwa cikin tarko,

23. inda kibiya za ta soke zuciyarta. Yana kama da tsuntsun da yake zuwa cikin tarko, bai kuwa sani ransa yana cikin hatsari ba.

24. Yanzu fa 'ya'yana, ku kasa kunne gare ni, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa.

Karanta cikakken babi K. Mag 7