Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 7:17-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Na yayyafa musu turaren mur da na aloyes da na kirfa.

18. Ka zo mu sha daɗin ƙauna, mu more dukan dare, mu yi farin ciki rungume da juna.

19. Mijina ba ya gida, ya yi tafiya mai nisa.

20. Ya tafi da kuɗi masu yawa, ba zai komo ba sai bayan mako biyu.”

21. Ta jarabce shi da kwarkwasarta, sai ya ba da kai ga daɗin bakinta.

22. Nan da nan ya bi ta kamar sā zuwa mayanka, kamar barewa tana tsalle zuwa cikin tarko,

23. inda kibiya za ta soke zuciyarta. Yana kama da tsuntsun da yake zuwa cikin tarko, bai kuwa sani ransa yana cikin hatsari ba.

24. Yanzu fa 'ya'yana, ku kasa kunne gare ni, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa.

25. Kada ku yarda irin wannan mace ta rinjayi zuciyarku, kada ku yi ta yawon nemanta.

26. Ita ce sanadin hallakar mutane da yawa, ta sa mutane da yawa mutuwa, har ba su ƙidayuwa.

27. Tafiya gidanta kuna kan hanya zuwa mutuwa ke nan, gajeruwar hanya ce zuwa lahira.

Karanta cikakken babi K. Mag 7