Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 6:9-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Har yaushe rago zai yi ta ɓalɓalcewa? Yaushe zai farka?

10. Yakan ce, “Bari in ɗan ruruma, in naɗa hannuwana in shaƙata.”

11. Amma lokacin da yake sharar barci, tsiya za ta auka masa kamar ɗan fashi da makamai.

12. Sakarkari, wato mugaye sukan yi ta baza jita-jita.

13. Sukan yi ƙyifce, ko su yi nuni don su yaudare ka.

14. A kowane lokaci suna shirya mugunta a kangararren hankalinsu, suna kuta tashin hankali ko'ina.

15. Saboda wannan masifa za ta fāɗa musu farat ɗaya ba makawa, za a yi musu mummunan raini.

16-19. Akwai abu shida, i, har bakwai ma, waɗanda Ubangiji yake ƙi, waɗanda ba zai haƙura da su ba,duban raini,harshe mai faɗar ƙarya,hannuwan da suke kashe marasa laifi,kwanyar da take tunane-tunanen mugayen dabaru,mutum mai gaggawar aikata mugunta,mai yawan shaidar zur,mutum mai ta da fitina a tsakanin abokai.

20. Ɗana, ka yi abin da mahaifinka ya faɗa maka, kada ka manta da koyarwar mahaifiyarka.

21. Kullum ka kiyaye abin da suke faɗa maka, ka kulle su kuma a zuciyarka.

22. Koyarwarsu za ta bi da kai sa'ad da kake tafiya, ta kiyaye ka da dare, ta kuma ba ka shawara da rana.

23. Doka da abubuwan da take koyarwa haske ne mai haskakawa. Tsautawa tana iya koya maka zaman duniya.

24. Za ta tsare ka daga mugayen mata, daga kalmomin alfasha da suke fitowa daga bakin matan waɗansu.

25. Kada kyansu ya jarabce ka, kada ka faɗa cikin tarkon feleƙensu.

26. Mutum ta dalilin karuwa zai sha hasarar abin da ya mallaka duka ta wurin zina.

27. Ka iya rungumar wuta a ƙirjinka sa'an nan ka ce ba za ta ƙone tufafinka ba?

28. Ka iya tafiya a kan garwashi sa'an nan ka ce ƙafafunka ba za su ƙone ba?

29. Haka yake da mutumin da ya kwana da matar wani. Duk wanda ya aikata wannan, zai sha wahala.

30. Mutane ba sukan raina wanda ya saci abinci don yana jin yunwa ba,

Karanta cikakken babi K. Mag 6