Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 6:24-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Za ta tsare ka daga mugayen mata, daga kalmomin alfasha da suke fitowa daga bakin matan waɗansu.

25. Kada kyansu ya jarabce ka, kada ka faɗa cikin tarkon feleƙensu.

26. Mutum ta dalilin karuwa zai sha hasarar abin da ya mallaka duka ta wurin zina.

27. Ka iya rungumar wuta a ƙirjinka sa'an nan ka ce ba za ta ƙone tufafinka ba?

28. Ka iya tafiya a kan garwashi sa'an nan ka ce ƙafafunka ba za su ƙone ba?

29. Haka yake da mutumin da ya kwana da matar wani. Duk wanda ya aikata wannan, zai sha wahala.

30. Mutane ba sukan raina wanda ya saci abinci don yana jin yunwa ba,

31. duk da haka in an kama shi, sai ya biya diyya sau bakwai, tilas kuwa ya ba da dukan abin da yake da shi.

32. Amma mazinaci marar hankali ne, gama hallaka kansa yake yi.

33. Zai sha dūka, a wulakanta shi, zai dawwama cikin kunya.

34. Hasalar miji mai kishi babu irinta, ramawarsa ba dama.

35. Ba zai karɓi biya ba, ba kyautar da za a yi masa wadda za ta kwantar da fushinsa.

Karanta cikakken babi K. Mag 6