Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 6:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ɗana, ka taɓa yin alkawari ka ɗaukar wa wani lamuni?

2. Maganganunka sun taɓa kama ka, ko alkawaranka sun taɓa zamar maka tarko?

3. To, ɗana, kana cikin ikon wannan mutum, amma ga yadda za ka yi ka fita, sheƙa zuwa wurinsa, ka roƙe shi ya sake ka.

4. Kada ka yarda ka yi barci ko ka huta.

5. Ka fita daga cikin tarkon kamar tsuntsu ko barewar da ta tsere wa maharbi.

6. Bari ragwaye su yi koyi da tururuwa.

7. Ba su da shugaba, ba su da sarki, ko mai mulki,

8. amma da kaka sukan tanada wa kansu abinci, domin kwanakin bazara.

9. Har yaushe rago zai yi ta ɓalɓalcewa? Yaushe zai farka?

10. Yakan ce, “Bari in ɗan ruruma, in naɗa hannuwana in shaƙata.”

11. Amma lokacin da yake sharar barci, tsiya za ta auka masa kamar ɗan fashi da makamai.

12. Sakarkari, wato mugaye sukan yi ta baza jita-jita.

Karanta cikakken babi K. Mag 6