Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 5:3-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Leɓunan matar wani, mai yiwuwa ne, su yi zaƙi kamar zuma, sumbace-sumbacenta kuma su fi man zaitun taushi.

4. Amma bayan an gama duka, ba abin da za ta bar maka sai baƙin ciki, da azaba.

5. Za ta gangara da kai zuwa lahira, hanyar da take bi hanyar mutuwa ce.

6. Ba a kan hanyar rai take ba, tana ragaita nesa da hanyar, amma kai ba ka ankara ba.

7. 'Ya'yana, ku kasa kunne gare ni yanzu, kada ko kusa ku manta da abin da nake faɗa.

8. Ku yi nesa da irin wannan mace! Kada ku yarda ku yi ko kusa da ƙofarta!

9. Idan kuwa kun yi, girmamawar da ake yi muku za ta zama ta waɗansu. Za ku yi mutuwar ƙuruciya ta hannun mutane marasa imani.

10. Hakika, baƙi za su kwashe dukan dukiyarku, abin da kuka sha wahalar samu kuma zai zama rabon wani dabam.

Karanta cikakken babi K. Mag 5