Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 5:13-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ban kasa kunne ga malamaina ba. Ban mai da hankalina gare su ba.

14. Farat ɗaya sai aka kunyatar da ni a bainar jama'a.”

15. Ka yi aminci ga matarka, ka ƙaunace ta ita kaɗai.

16. Idan kuma waɗansu mata sun haifa maka 'ya'ya, 'ya'yan nan ba za su yi maka wani amfani ba.

17. 'Ya'yanka za su yi girma su taimake ka, ba na baƙi ba.

18. Saboda haka ka yi farin ciki tare da matarka, ka yi murna da budurwa da ka auro,

19. kyakkyawa mai kyan gani kamar barewa. Bari kyanta ya ɗau hankalinka. Bari ƙaunarta ta kewaye ka.

20. Ɗana, don me za ka fi son matar wani? Don me za ka bar matar wani ta lallame ka da daɗin bakinta?

21. Ubangiji yana ganin dukan abin da kake yi. Inda ka shiga duk yana kallonka.

22. Zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi.

23. Yakan mutu saboda rashin kamewarsa, cikakkiyar wautarsa za ta kai shi kabarinsa.

Karanta cikakken babi K. Mag 5