Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 5:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ɗana, ka mai da hankali, ka kasa kunne ga hikimata da basirata.

2. Sa'an nan ne za ka san yadda za ka yi kome daidai, kalmominka za su nuna kana da ilimi.

3. Leɓunan matar wani, mai yiwuwa ne, su yi zaƙi kamar zuma, sumbace-sumbacenta kuma su fi man zaitun taushi.

4. Amma bayan an gama duka, ba abin da za ta bar maka sai baƙin ciki, da azaba.

5. Za ta gangara da kai zuwa lahira, hanyar da take bi hanyar mutuwa ce.

6. Ba a kan hanyar rai take ba, tana ragaita nesa da hanyar, amma kai ba ka ankara ba.

7. 'Ya'yana, ku kasa kunne gare ni yanzu, kada ko kusa ku manta da abin da nake faɗa.

8. Ku yi nesa da irin wannan mace! Kada ku yarda ku yi ko kusa da ƙofarta!

Karanta cikakken babi K. Mag 5