Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 4:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Samun hikima shi ne mafificin abin da za ka yi. Kome za ka samu dai, ka sami basira.

8. Ka ƙaunaci hikima, za ta girmama ka. Ka rungume ta, za ta kawo maka daraja.

9. Za ta zamar maka rawanin daraja.”

10. Ɗana, ka kasa kunne gare ni. Ka ɗauki abin da nake faɗa maka, muhimmin abu ne, za ka yi tsawon rai.

11. Gama na koya maka hikima da hanyar zama mai kyau.

12. Idan ka yi tafiya da hikima ba abin da zai tsare maka hanya, sa'ad da kake gudu ba za ka yi tuntuɓe ba.

13. Kullum ka tuna da abin da ka koya, iliminka shi ne ranka, ka lura da shi da kyau.

14. Kada ka tafi inda mugaye suke tafiya, kada ka bi gurbin mugaye.

15. Kada ka yi mugunta! Ka nisance ta! Ka ƙi ta, yi tafiyarka.

16. Mugaye ba su iya yin barci, sai sun aikata ɓarna. Ba su barci sai sun cuci wani.

17. Mugunta da ta'adi kamar ci da sha suke a gare su.

Karanta cikakken babi K. Mag 4