Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 4:19-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare. Sukan fāɗi, amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba.

20. Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa. Ka kasa kunne ga kalmomina.

21. Kada ka kuskura su rabu da kai, ka tuna da su, ka ƙaunace su.

22. Za su ba da rai da lafiya ga dukan wanda ya fahimce su.

23. Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja.

24. Kada ka faɗi kowane abu da yake ba na gaskiya ba, kada wani abu ya haɗa ka da ƙarya, ko maganganun ruɗawa.

25. Ka duba gaba sosai gabanka gaɗi, ba tsoro.

26. Ka tabbata ka san abin da kake yi, duk abin da kake yi kuma zai zama daidai.

27. Ka rabu da mugunta ka yi tafiyarka sosai, kada ka kauce ko da taki ɗaya daga hanyar da take daidai.

Karanta cikakken babi K. Mag 4