Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 4:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. 'Ya'yana ku kasa kunne ga koyarwar mahaifinku. Ku mai da hankali, za ku zama haziƙai.

2. Abin da nake koya muku, abu mai kyau ne, saboda haka ku tuna da shi duka.

3. Sa'ad da nake ɗan yaro tilo a wurin iyayena,

4. mahaifina yakan koya mini, yakan ce, “Ka tuna da abin da nake faɗa maka, kada ka manta. Ka yi abin da na faɗa maka za ka rayu.

5. Ka nemi hikima da basira! Kada ka manta ko ka ƙyale abin da na faɗa.

6. Kada ka rabu da hikima, gama za ta kiyaye ka, ka ƙaunace ta, za ta kiyaye lafiyarka.

7. Samun hikima shi ne mafificin abin da za ka yi. Kome za ka samu dai, ka sami basira.

8. Ka ƙaunaci hikima, za ta girmama ka. Ka rungume ta, za ta kawo maka daraja.

9. Za ta zamar maka rawanin daraja.”

10. Ɗana, ka kasa kunne gare ni. Ka ɗauki abin da nake faɗa maka, muhimmin abu ne, za ka yi tsawon rai.

11. Gama na koya maka hikima da hanyar zama mai kyau.

12. Idan ka yi tafiya da hikima ba abin da zai tsare maka hanya, sa'ad da kake gudu ba za ka yi tuntuɓe ba.

Karanta cikakken babi K. Mag 4