Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 31:20-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Takan yi wa matalauta da masu fatara karamci.

21. Ba ta jin tsoron lokacin sanyi gama 'ya'yanta duka suna da tufafi masu ƙauri.

22. Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa, tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.

23. Mijinta sananne ne a dandali, sa'ad da yake zaune tare da dattawan gari.

24. Takan yi riguna na lilin ta sayar, takan kuma sayar wa fatake da abin ɗamara.

25. Wadata da mutunci su ne suturarta. Ba ta jin tsoron tsufa.

26. Tana magana da hikima. Koyarwarta ta alheri ce.

27. Tana lura da al'amuran 'ya'yanta da kyau. Ba ruwanta da ƙyuya.

28. 'Ya'yanta sukan tashi su gode mata, mijinta kuma yana yabonta.

29. Ya ce, “Mata da yawa sun yi abin yabo, amma ke kin fi su duka.”

30. Kayan tsari da jamali duk banza ne, amma mace mai tsoron Ubangiji, ita ce abar yabo.

31. A yi mata cikakken yabo saboda ayyukanta, za a yabi ayyukanta a dandali.

Karanta cikakken babi K. Mag 31