Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 31:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan ita ce maganar sarki Lamuwel wadda uwarsa ta koya masa.

2. “Mene ne, ɗana? Mene ne, ya ɗana ne cikina? Mene ne, ɗana na wa'adi?

3. Kada ka ba da ƙarfinka ga mata, kada kuwa ka mai da hankali gare su, waɗanda suke hallaka sarakuna.

4. Bai dace ba, ya Lamuwel, bai dace ba ko kaɗan, sarakuna su sha ruwan inabi, ko masu mulki su yi marmarin barasa,

5. don kada su sha su manta da doka, su kuma kauce wa gaskiya a shari'ar waɗanda aka zalunta.

6. A ba da barasa ga wanda yake cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi kuma ga waɗanda suke cikin ɓacin rai.

7. Bari ya sha don ya manta da talaucinsa, don kada kuma ya ƙara tunawa da ɓacin ransa.

8. “Ka yi magana domin bebaye, domin kuma hakkin dukan waɗanda ba su da wani mataimaki.(1Sam 19.4; Ayu 29.12-17)

9. Ka yi magana dominsu, ka yi shari'ar adalci, ka kiyaye hakkin matalauta da masu bukata.”

10. Wa yake iya samun cikakkiyar mace? Darajarta ta fi ta lu'ulu'ai.

11. Mijinta yakan amince da ita, ba kuwa zai yi hasara ba.

12. Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakinta.

Karanta cikakken babi K. Mag 31