Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 30:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko?Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa?Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa?Wa kuma ya kafa iyakar duniya?Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa?Hakika ka sani!

5. “Kowace maganar Allah takan tabbata. Shi garkuwa ne ga waɗanda suke fakewa a wurinsa.

6. Kada ka yi ƙari a kan maganarsa, don kada ya tsauta maka, a kuma bayyana kai maƙaryaci ne.”

7. Abu biyu na roƙe ka, kada ka hana mini su kafin in mutu.

8. Ka kawar da ƙarya nesa da ni. Kada ka ba ni talauci ko dukiya, sai dai ka ba ni abinci daidai da bukatata,

9. don kada in wadata, har in yi musunka, in ce, “Wane ne Ubangiji?” Kada kuwa in yi talauci har in yi sata in saɓi sunan Allahna.

Karanta cikakken babi K. Mag 30