Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 3:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kada ka yarda ka rabu da biyayya da aminci, ka ɗaura su a wuyanka, ka rubuta su kuma a zuciyarka.

4. Idan ka yi wannan kuwa, Allah zai yi murna da kai. Za ka yi nasara cikin hulɗar da kake yi da mutane.

5. Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani.

6. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.

7. Sam, kada ka yarda ka ɗauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata mugunta.

8. Idan ka kiyaye wannan, zai zama maka kamar magani mai kyau, ya warkar da raunukanka, ya kuma sawwaƙe maka azabar da kake sha.

9. Ka girmama Ubangiji ta wurin miƙa masa hadaya daga mafi kyau na amfanin gonarka.

10. Idan ka yi haka rumbunanka za su cika da hatsi. Za ka sami ruwan inabi mai yawa, har ka rasa wurin da za ka zuba shi duka.

11. Ɗana, sa'ad da Ubangiji ya tsauta maka ka mai da hankali sosai, ka kuma yarda da gargaɗinsa.

12. Ubangiji yana tsauta wa waɗanda yake ƙauna. Kamar yadda mahaifi yakan tsauta wa ɗan da yake fāriya da shi.

13. Mai farin ciki ne mutumin da ya zama mai hikima, ya kuma sami fahimi.

14. Yana da riba mai yawan gaske fiye da ta azurfa, tamaninta a gare ka ya fi na zinariya.

15. Tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai, ya kuma fi kowane irin abin da kake so tamani.

Karanta cikakken babi K. Mag 3