Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 3:18-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Masu farin ciki ne waɗanda suka sami hikima, hikima za ta ba su rai kamar yadda itace yakan ba da 'ya'ya.

19. Ubangiji ya halicci duniya ta wurin hikimarsa,Ya shimfiɗa sararin sama a inda yake ta wurin saninsa.

20. Hikimarsa ta sa ruwan koguna ya yi gudu,Gizagizai kuwa su zubo da ruwa bisa duniya.

21. Ɗana ka riƙe hikimarka da basirarka. Ko kusa kada ka bari su rabu da kai.

22. Za su tanada maka rai, rai mai daɗi da farin ciki.

23. Za ka bi hanyarka lafiya lau, ba ko tuntuɓe.

24. Ba za ka ji tsoro, sa'ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare.

25. Ba za ka damu da masifar da za ta auko farat ɗaya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri.

26. Ubangiji zai kiyaye ka. Ba zai bari ka fāɗa cikin tarko ba.

27. Ka yi wa masu bukata alheri a duk lokacin da kake iyawa.

28. Sam, kada ka ce wa maƙwabcinka ya dakata sai gobe, idan dai kana iya taimakonsa yanzu.

29. Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, gama yana zaune kusa da kai, yana kuwa amincewa da kai.

30. Kada ka yi jayayya ba dalili da wanda bai taɓa cutarka ba.

31. Kada ka ji kishin masu ta da zaune tsaye, ko ka yi sha'awar aikata ayyukansu,

32. gama Ubangiji yana ƙin mutanen da suke aikata mugunta, amma yakan rungumi adalai ya amince da su.

33. Ubangiji yakan la'antar da gidajen masu mugunta, amma yakan sa wa gidajen adalai albarka.

34. Ba ruwansa da masu girmankai, amma masu tawali'u sukan sami tagomashi a wurinsa.

35. Mutane masu hikima za su sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.

Karanta cikakken babi K. Mag 3