Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 3:11-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ɗana, sa'ad da Ubangiji ya tsauta maka ka mai da hankali sosai, ka kuma yarda da gargaɗinsa.

12. Ubangiji yana tsauta wa waɗanda yake ƙauna. Kamar yadda mahaifi yakan tsauta wa ɗan da yake fāriya da shi.

13. Mai farin ciki ne mutumin da ya zama mai hikima, ya kuma sami fahimi.

14. Yana da riba mai yawan gaske fiye da ta azurfa, tamaninta a gare ka ya fi na zinariya.

15. Tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai, ya kuma fi kowane irin abin da kake so tamani.

16. Hikima takan tsawanta ranka, ta kuma ba ka dukiya da daraja.

17. Hikima takan sa ka ji daɗin zama, ta kuma bi da kai lafiya a zamanka.

18. Masu farin ciki ne waɗanda suka sami hikima, hikima za ta ba su rai kamar yadda itace yakan ba da 'ya'ya.

19. Ubangiji ya halicci duniya ta wurin hikimarsa,Ya shimfiɗa sararin sama a inda yake ta wurin saninsa.

20. Hikimarsa ta sa ruwan koguna ya yi gudu,Gizagizai kuwa su zubo da ruwa bisa duniya.

21. Ɗana ka riƙe hikimarka da basirarka. Ko kusa kada ka bari su rabu da kai.

22. Za su tanada maka rai, rai mai daɗi da farin ciki.

23. Za ka bi hanyarka lafiya lau, ba ko tuntuɓe.

24. Ba za ka ji tsoro, sa'ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare.

25. Ba za ka damu da masifar da za ta auko farat ɗaya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri.

26. Ubangiji zai kiyaye ka. Ba zai bari ka fāɗa cikin tarko ba.

27. Ka yi wa masu bukata alheri a duk lokacin da kake iyawa.

28. Sam, kada ka ce wa maƙwabcinka ya dakata sai gobe, idan dai kana iya taimakonsa yanzu.

29. Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, gama yana zaune kusa da kai, yana kuwa amincewa da kai.

30. Kada ka yi jayayya ba dalili da wanda bai taɓa cutarka ba.

Karanta cikakken babi K. Mag 3