Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 3:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ɗana kada ka manta da abin da na koya maka. Kullum ka tuna da abin da na faɗa maka ka yi.

2. Koyarwata za ta ba ka tsawon rai da wadata.

3. Kada ka yarda ka rabu da biyayya da aminci, ka ɗaura su a wuyanka, ka rubuta su kuma a zuciyarka.

4. Idan ka yi wannan kuwa, Allah zai yi murna da kai. Za ka yi nasara cikin hulɗar da kake yi da mutane.

5. Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani.

6. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.

7. Sam, kada ka yarda ka ɗauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata mugunta.

Karanta cikakken babi K. Mag 3