Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 29:5-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Mutum wanda yake yi wa maƙwabcinsa daɗin baƙi yana kafa wa kansa tarko.

6. Laifin mugun zai zama tarko a gare shi, amma adali zai raira waƙa, ya yi farin ciki.

7. Adali yana sane da hakkin matalauta, amma mugun bai san wannan ba.

8. Ashararai sukan sa wa birni wuta, amma masu hikima sukan kwantar da hasala.

9. Idan gardama ta shiga tsakanin mai hikima da wawa, sai wawa ya yi ta fushi, ko kuwa ya yi ta dariya, gardamar dai ba za ta ƙare ba.

10. Mutane masu kisankai suna ƙin amintaccen mutum, amma adalai za su kiyaye ransa.

11. Wawa yakan nuna fushinsa ko yaushe, amma mutum mai hikima yakan kanne fushinsa.

12. Idan mai mulki yana kasa kunne ga maganganun ƙarya, dukan ma'aikatansa za su zama maƙaryata.

Karanta cikakken babi K. Mag 29