Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 29:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Wawa yakan nuna fushinsa ko yaushe, amma mutum mai hikima yakan kanne fushinsa.

12. Idan mai mulki yana kasa kunne ga maganganun ƙarya, dukan ma'aikatansa za su zama maƙaryata.

13. Matalauci da azzalumi suna tarayya a abu ɗaya, wato dukansu Ubangiji ne yake ba su ganin gari.

14. Idan sarki yana yi wa talakawa shari'ar gaskiya, zai daɗe yana mulki.

15. Horo da tsautawa suna ba da hikima, amma yaron da aka sangarta zai jawo wa mahaifiyarsa kunya.

16. Sa'ad da mugaye suke mulki, laifofi suka ƙaru, amma adalai za su ga faɗuwar waɗannan mutane.

17. Ka hori ɗanka zai daɗaɗa maka rai, ya kuma faranta maka zuciya.

18. Inda ba a bin faɗar Allah, jama'a za su kangare, amma mai farin ciki ne wanda yake kiyaye dokar Allah.

Karanta cikakken babi K. Mag 29