Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 29:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wanda ake ta tsauta wa a kai a kai, amma ya taurare, ba makawa tasa ta ƙare farat ɗaya.

2. Sa'ad da masu adalci suke mulki, jama'a sukan yi murna, amma sa'ad da mugaye suke mulki, jama'a sukan yi nishi.

3. Wanda yake ƙaunar hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa.Amma wanda yake abuta da karuwai zai lalatar da dukiyarsa.

4. Sarkin da yake aikata adalci ƙasarsa za ta yi ƙarƙo, amma wanda yake karɓar rashawa zai lalatar da ƙasar.

5. Mutum wanda yake yi wa maƙwabcinsa daɗin baƙi yana kafa wa kansa tarko.

6. Laifin mugun zai zama tarko a gare shi, amma adali zai raira waƙa, ya yi farin ciki.

7. Adali yana sane da hakkin matalauta, amma mugun bai san wannan ba.

8. Ashararai sukan sa wa birni wuta, amma masu hikima sukan kwantar da hasala.

Karanta cikakken babi K. Mag 29