Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 27:5-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Gara ka tsauta wa mutum a fili da ka bar shi ya zaci ba ka kula da shi ba sam.

6. Aboki aboki ne ko da ya cuce ka, amma maƙiyi ko ya rungume ka kada ka sake!

7. Wanda ya ƙoshi ba zai ko kula da zuma ba, amma wanda yake jin yunwa abinci mai ɗaci zaƙinsa yake ji.

8. Mutumin da ya bar gida yana kama da tsuntsun da ya bar sheƙarsa.

9. Turare da man ƙanshi sukan sa ka ji daɗi, haka abuta ta ainihi takan ƙara maka ƙarfi.

10. Kada ka manta da abokanka, ko abokan mahaifinka. Idan kana shan wahala kada ka nemi taimako wurin ɗan'uwanka. Maƙwabci na kusa yana iya taimakonka fiye da ɗan'uwan da yake nesa.

11. Ɗana, ka zama mai hikima, ni kuwa zan yi farin ciki, zan iya amsa kowace irin sūkar da wani zai yi mini.

12. Mutum mai hankali yakan hango hatsari ya kauce masa, amma mutumin da ba shi da kula, yakan kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.

13. Ka karɓe tufar wanda ya zamar wa baƙo lamuni, da kuma wanda ya zama lamunin karuwa.

14. In ka farkar da abokinka da babbar murya tun da sassafe, daidai ne da zaginsa.

15. Mace mai mita kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa.

16. Kaƙa za ka iya sa ta ta kame bakinta? Ka taɓa ƙoƙarin tsai da iska? Ko kuwa ka taɓa ƙoƙarin dintsi mai a tafin hannunka?

17. Daga wurin mutane mutane suke koyo, kamar yadda a kan wasa ƙarfe da ƙarfe.

18. Ka lura da itacen ɓaure, zai yi 'ya'ya ka ci. Baran da ya lura da maigidansa za a girmama shi.

Karanta cikakken babi K. Mag 27