Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 27:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kada ka yi fāriya a kan abin da za ka yi gobe domin ba ka san abin da zai faru daga yanzu zuwa gobe ba.

2. Bari waɗansu su yabe ka ko da baƙi ne, faufau kada ka yabi kanka.

3. Dutse da yashi suna da nauyi ƙwarai, amma nauyin wahalar da wawa zai haddasa ya fi nasu duka.

4. Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma duk da haka bai kai ga kishi ba.

5. Gara ka tsauta wa mutum a fili da ka bar shi ya zaci ba ka kula da shi ba sam.

6. Aboki aboki ne ko da ya cuce ka, amma maƙiyi ko ya rungume ka kada ka sake!

7. Wanda ya ƙoshi ba zai ko kula da zuma ba, amma wanda yake jin yunwa abinci mai ɗaci zaƙinsa yake ji.

8. Mutumin da ya bar gida yana kama da tsuntsun da ya bar sheƙarsa.

9. Turare da man ƙanshi sukan sa ka ji daɗi, haka abuta ta ainihi takan ƙara maka ƙarfi.

10. Kada ka manta da abokanka, ko abokan mahaifinka. Idan kana shan wahala kada ka nemi taimako wurin ɗan'uwanka. Maƙwabci na kusa yana iya taimakonka fiye da ɗan'uwan da yake nesa.

Karanta cikakken babi K. Mag 27