Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 26:6-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Mutumin da ya sa wawa ya isar masa da saƙo ya datse ƙafafunsa, yana nemar wa kansa wahala.

7. Wawa yakan yi amfani da karin magana kamar yadda tauyayyen mutum yake amfani da ƙafafunsa.

8. Wanda ya yabi wawa yana kama da wanda ya ɗaura dutse a majajjawa.

9. Karin magana a bakin wawa kamar sukar ƙaya ce a hannun mai maye.

10. Wanda ya ɗauki wawa aiki yana cutar duk wanda aikin ya shafa.

11. Wawan da yake maimaita aikin wautarsa yana kama da kare mai yin amai ya koma ya tanɗe.

12. Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.

13. Don me malalaci yakan kasa fita daga gida? Zaki yake tsoro?

14. Malalaci yana ta jujjuyawa a gadonsa kamar yadda ƙyauren ƙofa take juyawa.

15. Malalaci yana sa hannu cikin ƙwaryar abinci, amma ya kāsa kaiwa bakinsa.

16. Malalaci yana ganin kansa mai hikima ne fiye da mutum bakwai waɗanda suke da dalilai a kan ra'ayinsu.

17. Mutumin da ya tsoma baki cikin jayayyar da ba ta shafe shi ba sa'ad da yake wucewa, yana kama da mutum wanda yake kama kare a kunne.

18-19. Mutum wanda yakan ruɗi maƙwabcinsa sa'an nan ya ce, wasa yake yi kawai, yana kama da mahaukaci wanda yake wasa da wuta, da kibau, da mutuwa.

20. Idan ba itace wuta takan mutu, haka kuma idan ba mai gulma ba za a yi jayayya ba.

Karanta cikakken babi K. Mag 26