Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 26:13-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Don me malalaci yakan kasa fita daga gida? Zaki yake tsoro?

14. Malalaci yana ta jujjuyawa a gadonsa kamar yadda ƙyauren ƙofa take juyawa.

15. Malalaci yana sa hannu cikin ƙwaryar abinci, amma ya kāsa kaiwa bakinsa.

16. Malalaci yana ganin kansa mai hikima ne fiye da mutum bakwai waɗanda suke da dalilai a kan ra'ayinsu.

17. Mutumin da ya tsoma baki cikin jayayyar da ba ta shafe shi ba sa'ad da yake wucewa, yana kama da mutum wanda yake kama kare a kunne.

18-19. Mutum wanda yakan ruɗi maƙwabcinsa sa'an nan ya ce, wasa yake yi kawai, yana kama da mahaukaci wanda yake wasa da wuta, da kibau, da mutuwa.

20. Idan ba itace wuta takan mutu, haka kuma idan ba mai gulma ba za a yi jayayya ba.

21. Kamar yadda gawayi yake ga garwashin wuta, itace kuma ga wuta, haka mai gardama yake ga jayayya.

Karanta cikakken babi K. Mag 26