Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 25:16-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Kada ka kuskura ka sha zuma gaba da kima, in ya yi maka yawa za ka yi hararwa.

17. Kada ka cika ziyartar maƙwabcinka, ko zai gaji da kai har ya ƙi ka.

18. Mutumin da yakan faɗi ƙarairayi a kan maƙwabcinsa, shi kamar kakkaifan takobi ne, ko kulki, ko kibiya mai tsini.

19. Dogara ga marar aminci a lokacin hargitsi, kamar ƙoƙarin yin tauna da ruɓaɓɓun haƙora ne, ko yin tafiya da mai gurguwar ƙafa,

20. ko kuma ka yi ƙoƙarin jin ɗumi ta wurin tuɓe tufafinka a ranar da ake sanyi.Raira waƙa ga mai baƙin ciki kamar marmasa gishiri a kan rauni ne.

21. Idan maƙiyinka yana jin yunwa ka cishe shi, idan yana jin ƙishi ka ba shi abin sha.

22. Za ka sa ya sha kunya, Ubangiji kuma zai sāka maka.

23. Iskar arewa takan kawo ruwan sama, haka kuma jita-jita takan kawo fushi.

24. Gara zama a saƙo da zama a gida ɗaya tare da mata mai mita.

25. Jin labari mai daɗi wanda ba ka zato, yana kamar shan ruwan sanyi ne a sa'ad da ka sha rana kana jin ƙishi.

26. Mutumin kirki wanda yakan yarda da mugun yana tunasshe ka da ƙazantattun maɓuɓɓuga ko rijiya mai dafi.

27. Kamar yadda shan zuma da yawa ba shi da kyau a gare ka, haka kuma ƙoƙarin neman yabo mai yawa yake.

28. Idan ba ka iya danne fushinka ba, ka zama mai kasala kamar birnin da ba shi da garuka, yana buɗe don a faɗa masa.

Karanta cikakken babi K. Mag 25