Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 25:12-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Faɗakarwar da mutumin da ya gogu da al'amuran duniya ya yi ga wanda yake da niyya ya kasa kunne, tamaninta ya fi na zoben zinariya, ko kayan ado da aka yi da zinariya tsantsa.

13. Amintaccen manzo yakan wartsakar da wanda ya aike shi, kamar ruwan sanyi yake a lokacin zafi.

14. Mutanen da suke yin alkawari, ba su cikawa, kamar holoƙo suke, hadirin kaka.

15. Rinjayen da aka yi cikin haƙuri yakan rushe ƙaƙƙarfar tsayayya, har ma yakan i wa masu ƙarfin gaske.

16. Kada ka kuskura ka sha zuma gaba da kima, in ya yi maka yawa za ka yi hararwa.

17. Kada ka cika ziyartar maƙwabcinka, ko zai gaji da kai har ya ƙi ka.

18. Mutumin da yakan faɗi ƙarairayi a kan maƙwabcinsa, shi kamar kakkaifan takobi ne, ko kulki, ko kibiya mai tsini.

19. Dogara ga marar aminci a lokacin hargitsi, kamar ƙoƙarin yin tauna da ruɓaɓɓun haƙora ne, ko yin tafiya da mai gurguwar ƙafa,

20. ko kuma ka yi ƙoƙarin jin ɗumi ta wurin tuɓe tufafinka a ranar da ake sanyi.Raira waƙa ga mai baƙin ciki kamar marmasa gishiri a kan rauni ne.

21. Idan maƙiyinka yana jin yunwa ka cishe shi, idan yana jin ƙishi ka ba shi abin sha.

22. Za ka sa ya sha kunya, Ubangiji kuma zai sāka maka.

23. Iskar arewa takan kawo ruwan sama, haka kuma jita-jita takan kawo fushi.

24. Gara zama a saƙo da zama a gida ɗaya tare da mata mai mita.

25. Jin labari mai daɗi wanda ba ka zato, yana kamar shan ruwan sanyi ne a sa'ad da ka sha rana kana jin ƙishi.

Karanta cikakken babi K. Mag 25