Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 23:3-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kada ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da yake gabanku, zai yiwu wayo yake so ya yi maka.

4. Ka zama mai isasshiyar hikima, kada ka gajiyar da kanka garin ƙoƙarin neman dukiya.

5. Kuɗinka sun iya ƙarewa kamar ƙyiftawar ido, kamar suna da fikafikai su tashi kamar gaggafa.

6. Kada ka ci abincin marowaci, ko ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da ya sa a gabanka.

7. Zai ce, “Bari a ƙara maka,” amma ba haka yake nufi ba. Kamar gashi yake a cikin maƙogwaronka.

8. Za ka harar da abin da ka ci, dukan daɗin bakinka zai tafi a banza.

9. Kada ka yi wa wawa magana irin ta haziƙai, gama ba zai yaba da maganarka ba.

10. Kada ka kuskura ka kawar da shaidar iyaka, ko ka ƙwace gonar marayu.

11. Ubangiji Mai Iko shi ne kāriyarsu, shi zai yi magana dominsu.

12. Ka mai da hankali ga malaminka, ka koyi dukan abin da kake iyawa.

13. Kada ka bar yaro ba horo, gama ko ka duke shi ba za a kashe shi ba.

14. Lalle ne za ka ceci ransa.

Karanta cikakken babi K. Mag 23