Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 22:20-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Na rubuta maka karin magana, suna ƙunshe da ilimi da kyakkyawar shawara.

21. Zan koya maka ainihin gaskiya, domin sa'ad da aka aike ka ka nemo ta, za ka iya kawo amsa daidai.

22. Kada ka ƙwari matalauci don ka fi shi, kada ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari'a.

23. Ubangiji zai yi magana dominsu a kan shari'ar da suke yi, ya nemi ran duk wanda yake neman rayukansu.

24. Kada ka yi abuta da mutane masu zafin fushi, ko masu zafin rai.

25. Mai yiwuwa ne ka koyi irin ɗabi'unsu, har ka kasa sākewa.

26. Kada ka yi alkawarin ɗaukar wa wani lamuni,

27. gama idan ka kāsa biya har gadonka ma za su ɗauke.

28. Kada ka kawar da shidar kan iyaka wadda kakanninka suka kafa.

29. Ka nuna mini mutumin da yake aiki mai kyau, ni kuwa in nuna maka mutumin da ya fi duka, wanda ya cancanci ya zauna tare da sarakuna.

Karanta cikakken babi K. Mag 22