Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 22:12-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ubangiji yana lura ya ga an riƙe gaskiya sosai ta wurin ƙin yarda da maganganun ƙarya.

13. Malalaci yakan yi zamansa a gida, yakan ce, “Zaki zai kama ni in na fita waje.”

14. Zina tarko ce, takan kama waɗannan waɗanda Ubangiji yake fushi da su.

15. Halin yara ne su yi wauta da waɗansu abubuwa na rashin kula, amma tsumagiya za ta koya musu abin da ya fi kyau.

16. Idan attajirai kake yi wa kyauta, kana kuma zaluntar matalauta don ka arzuta, kai kanka za ka talauce.

17. Ka kasa kunne zan koya maka abin da masu hikima suka faɗa, yi nazari a kan koyarwarsu.

18. Za ka yi murna in ka tuna da su, ka iya faɗarsu.

19. Ina so ka dogara ga Ubangiji, don haka zan faɗa maka su yanzu.

20. Na rubuta maka karin magana, suna ƙunshe da ilimi da kyakkyawar shawara.

21. Zan koya maka ainihin gaskiya, domin sa'ad da aka aike ka ka nemo ta, za ka iya kawo amsa daidai.

22. Kada ka ƙwari matalauci don ka fi shi, kada ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari'a.

23. Ubangiji zai yi magana dominsu a kan shari'ar da suke yi, ya nemi ran duk wanda yake neman rayukansu.

24. Kada ka yi abuta da mutane masu zafin fushi, ko masu zafin rai.

Karanta cikakken babi K. Mag 22