Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 21:21-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ka yi alheri ka yi aminci, za ka yi tsawon rai waɗansu kuma za su girmama ka, su yi maka abin da yake daidai.

22. Sarkin yaƙi mai wayo yakan ci birnin da jarumawa suke tsaro, ya rushe garun da suke taƙama da shi.

23. Idan ba ka so ka shiga wahala, ka lura da abin da kake faɗa.

24. Ba kalmar da ta fi “fāɗin rai” dacewa ga mutum mai girmankai, mai fāriya marar tunani.

25. Malalacin mutumin da ya ƙi yin aiki, kansa yake kashewa.

26. Duk abin da yake tunani dukan yini, shi ne a kan abin da yake so ya samu. Amma adali ko ta ƙaƙa yakan bayar da hannu sake.

27. Ubangiji yana ƙin hadayar da mugaye suka miƙa masa, tun ba wadda suka miƙa ta da mugun nufi ba.

28. Ba a gaskata shaidar maƙaryaci, amma mutumin da yakan yi tunani a kan al'amura, akan karɓi tasa.

29. Adali ya tabbatar da kansa, haka ma mugun mutum yakan yi da'awa, cewa shi ma ya tabbatar da kansa.

30. Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.

31. Kana iya shirya dawakai don zuwa yaƙi, amma nasara ta Ubangiji ce.

Karanta cikakken babi K. Mag 21