Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 21:15-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sa'ad da aka yi adalci mutanen kirki sukan yi murna, amma mugaye sukan yi baƙin ciki.

16. Mutuwa tana jiran wanda ya ƙi bin hanyar hankali.

17. Sa kai cikin nishaɗi, wato shan ruwan inabi, da cin abinci mai tsada, ba zai bar ka ka tara dukiya ba.

18. Wahalar da mugaye suke so su jawo wa mutanen kirki, za ta koma kansu.

19. Gara ka zauna a hamada, da ka zauna tare da mace mai mita, mai yawan kai ƙara.

20. Mutane masu hikima suna zaune da wadata da nishaɗi, amma wawaye da zarar sun sami kuɗi sukan kashe su nan da nan.

21. Ka yi alheri ka yi aminci, za ka yi tsawon rai waɗansu kuma za su girmama ka, su yi maka abin da yake daidai.

22. Sarkin yaƙi mai wayo yakan ci birnin da jarumawa suke tsaro, ya rushe garun da suke taƙama da shi.

23. Idan ba ka so ka shiga wahala, ka lura da abin da kake faɗa.

24. Ba kalmar da ta fi “fāɗin rai” dacewa ga mutum mai girmankai, mai fāriya marar tunani.

25. Malalacin mutumin da ya ƙi yin aiki, kansa yake kashewa.

26. Duk abin da yake tunani dukan yini, shi ne a kan abin da yake so ya samu. Amma adali ko ta ƙaƙa yakan bayar da hannu sake.

27. Ubangiji yana ƙin hadayar da mugaye suka miƙa masa, tun ba wadda suka miƙa ta da mugun nufi ba.

28. Ba a gaskata shaidar maƙaryaci, amma mutumin da yakan yi tunani a kan al'amura, akan karɓi tasa.

Karanta cikakken babi K. Mag 21