Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 21:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ne yake mallakar tunanin sarki a sawwaƙe kamar yadda yake yi da ruwan rafi.

2. Ko da a ce dukan abin da kake yi daidai ne, ka tuna fa Ubangiji ya san manufarka.

3. Ubangiji ya fi so ka yi abin da yake daidai, mai kyau kuma, fiye da ka miƙa masa hadayu.

4. Girmankai da fāriya suke bi da mugaye, wannan kuwa zunubi ne.

5. Yin shiri a tsanaki zai kai ka ga biyan bukatarka, idan kuwa ka cika gaggawa ba za ka sami abin da zai ishe ka ba.

6. Dukiyar da aka tara ta hanyar rashin gaskiya takan ƙare nan da nan, takan kuma kai ga mutuwa.

7. Mugaye, tasu ta ƙare saboda muguntarsu, gama sun ƙi yin abin da yake daidai.

8. Mutane masu laifi sukan bi ta karkatacciyar hanya, marasa laifi kuwa suna aikata abin da yake daidai.

9. Gara zama a saƙo da zama a gida ɗaya tare da mace mai mita.

10. Mugaye sun zaƙu su aikata mugunta, ba su yi wa kowa jinƙai.

11. Sa'ad da aka hukunta mai girmankai, ko marar tunani yakan koyi wani abu, mutum mai hikima yakan koyi abin da ake koya masa.

12. Adali ya san tunanin mugaye, yakan kuwa zama sanadin lalacewarsu.

13. Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.

Karanta cikakken babi K. Mag 21