Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 2:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Tsinkayarka da fahiminka za su tsare ka.

12. Za su hana ka aikata mugayen ayyuka, za su nisantar da kai daga mutane masu ta da hargitsi da irin maganganunsu,

13. mutane waɗanda suka bar zaman adalci don su zauna cikin duhun zunubi,

14. waɗanda suke jin daɗin yin laifi, suna nishaɗi cikin mugunta.

15. Ba za a dogara da su ba, ba kuwa za a iya amincewa da su ba.

16. Za a nisantar da kai daga mazinaciya, wadda take ƙoƙari ta lalatar da kai da daɗin bakinta,

17. marar aminci ga mijinta, wadda ta manta da tsarkakan alkawaran da ta ɗauka.

18. Idan ka tafi gidanta ka kama hanyar mutuwa. Tafiya can kama hanyar zuwa lahira ne.

19. Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa. Ba zai ƙara komowa ga hanyar rai ba.

20. Saboda haka dole ka bi hanyar da mutanen kirki suka bi, ka bi gurbin adalai.

21. Mutane adalai, masu kamewa, su ne za su zauna ƙasarmu.

22. Amma Allah zai fizge mugaye daga ƙasar, ya kuma tumɓuke masu zunubi kamar yadda ake tumɓuke shuke-shuke daga ƙasa.

Karanta cikakken babi K. Mag 2