Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 18:13-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ka saurara kafin ka amsa, idan kuwa ba ka yi ba, ka zama dakiki mai bankunya.

14. Sa zuciya ga rai yakan taimaki mutum sa'ad da yake ciwo, amma idan ya karai, to, tasa ta ƙare.

15. Mutane masu basira, a ko yaushe suna da himma, a shirye kuma suke domin su koya.

16. Kana so ka sadu da babban mutum? Ka kai masa kyauta, za ka gan shi a sawwaƙe.

17. Wanda ya fara mai da magana a majalisa yakan zama kamar shi ne mai gaskiya, sai abokin shari'arsa ya mai da tasa maganar tukuna.

18. Idan mutum biyu ƙarfafa suna jayayya da juna a gaban shari'a, kuri'a a asirce kaɗai take iya daidaita tsakaninsu.

19. Ɗan'uwan da ya ji haushinka zai gagare ka, idan ka yi faɗa da shi zai rufe maka ƙofarsa.

20. Bisa ga sakamakon hurcinka haka za ka rayu.

21. Abin da ka faɗa ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karɓi sakamakon maganarka.

22. Idan ka sami mace ka sami abu mai kyau, wannan alheri ne wanda Ubangiji ya yi maka.

23. Matalauci yakan yi roƙo da taushi, maganar matalauci rarrashi ne, amma attajiri yakan yi magana garas.

Karanta cikakken babi K. Mag 18