Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 17:2-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Bara mai wayo yakan sami iko a kan shashashan ɗan maigidansa, har ya sami rabo a cikin gādon.

3. Zinariya da azurfa da wuta ake gwada su, zuciyar ɗan adam kuwa Ubangiji ne yake gwada ta.

4. Mugaye sukan kasa kunne ga mugayen dabaru, maƙaryata kuma sukan kasa kunne ga ƙarairayi.

5. Wanda ya yi wa matalauci ba'a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka.

6. Tsofaffi suna fāriya da jikokinsu, kamar yadda samari suke alfarma da iyayensu maza.

7. Mutumin da yake kamili ba ya faɗar ƙarya, haka ma wawa ba zai faɗi wani abin kirki ba.

8. Waɗansu mutane suna tsammani cin rashawa yakan yi aiki kamar sihiri, sun gaskata zai iya yin kome.

9. Idan kana so mutane su so ka, ka riƙa yafe musu sa'ad da suka yi maka laifi. Mita takan raba abuta.

10. Mutum mai fasaha yakan koyi abu da yawa daga tsautawa ɗaya, fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.

Karanta cikakken babi K. Mag 17