Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 17:15-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Da wanda ya baratar da mugun da wanda ya kā da adali, duk abin ƙi suke ga Ubangiji.

16. Kashe kuɗi saboda ilimi ba shi da amfanin kome ga wawa, domin ba shi da tunani.

17. A ko yaushe abokai sukan nuna ƙaunarsu, 'yan'uwa kuma, ai, don su ɗauki nawayar juna suke.

18. Sai mutum marar tunani ne kaɗai zai ɗauki lamunin basusuwan maƙwabcinsa.

19. Shi wanda yake son zunubi, yana son wahala ke nan, wanda kuma yake yin fāriya a dukan lokaci yana neman tashin hankali ke nan.

20. Mutumin da yakan yi tunanin mugunta, ya kuma hurta ta, kada ya sa zuciya ga samun abin kirki, sai dai bala'i kaɗai.

21. Mahaifi wanda ɗansa yake yin abubuwan wauta, ba shi da kome sai ɓacin rai da baƙin ciki.

22. Kasancewa da murna yakan ba ka lafiya. Zama da baƙin rai dukan lokaci mutuwar tsaye ce.

23. Alƙalai marasa gaskiya suna cin hanci a ɓoye, sa'an nan ba za su aikata adalci ba.

24. Baligi da hikima yake aikinsa, amma wanda bai balaga ba, bai san abin da zai yi ba.

25. Wawan da yakan jawo wa mahaifinsa ɓacin rai, abin baƙin ciki yake ga mahaifiyarsa.

26. Ba daidai ba ne a ci marar laifi tara, yi wa mutumin kirki bulala kuwa rashin adalci ne.

27. Mutumin da ya tabbata yana da gaskiya ba zai cika yawan magana ba, natsattsen mutum yana da basira ƙwarai.

28. Banda haka ma, ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, mai basira.

Karanta cikakken babi K. Mag 17