Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 17:10-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Mutum mai fasaha yakan koyi abu da yawa daga tsautawa ɗaya, fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.

11. Mutuwa za ta zo wa mugaye kamar mugun manzo wanda a ko yaushe yana so ya kuta tashin hankali.

12. Gara mutum ya gamu da beyar ta mata wadda aka kwashe mata kwiyakwiyanta, da ka gamu da waɗansu wawaye suna aikin dakikancinsu.

13. Idan ka sāka alheri da mugunta, ba za ka iya raba gidanka da mugunta ba, faufau.

14. Mafarin jayayya kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, sai a tsai da ita tun ba ta haɓaka ba.

15. Da wanda ya baratar da mugun da wanda ya kā da adali, duk abin ƙi suke ga Ubangiji.

Karanta cikakken babi K. Mag 17