Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 16:17-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Mutumin kirki yana tafiya a hanyar da ta kauce wa mugunta, saboda haka ka kula da inda kake tafiya, za ta ceci ranka.

18. Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa.

19. Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu tawali'u, da ka zama ɗaya daga cikin masu girmankai, har da za ka sami rabo daga cikin ganimarsu.

20. Ka mai da hankali ga abin da aka koya maka, za ka yi nasara. Ka dogara ga Ubangiji, za ka yi farin ciki.

21. Mutum mai hikima, wanda ya isa mutum, akan san shi ta wurin haziƙancinsa, kamar yadda kalmominsa suke da daɗi, haka ma rinjayarsa take.

22. Hikima maɓuɓɓugar rai ce ga mai hikima, amma ɓata lokaci ne a yi ƙoƙarin koya wa dakikai.

23. Mai hikima yakan yi tunani kafin ya yi magana, abin da ya faɗa yakan yi rinjaye ƙwarai.

24. Kalmomi masu daɗi suna kama da zuma, suna da daɗin ɗanɗana, suna kuma da amfani domin lafiyarka.

25. Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.

26. Marmarin cin abinci yakan sa ɗan ƙodago ya yi aiki da ƙwazo, domin yana so ya ci ya ƙoshi.

27. Mutumin da yake jin daɗin yin mugunta yakan tafi yawon nemanta, mugayen maganganunsa ƙuna suke kamar wuta.

28. Mugaye sukan baza jita-jita, suna zuga tashin hankali, suna raba aminai.

29. Mutum mai ta da zaune tsaye yakan ruɗi abokansa, ya kai su ga bala'i.

Karanta cikakken babi K. Mag 16