Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 15:23-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Me ya fi wannan zama abin murna? Mutum ya sami maganar da take daidai a lokacin da ya dace!

24. Mutum mai hikima yakan kama hanya ya haura zuwa rai, ba ya bin hanyar da ta gangara zuwa mutuwa.

25. Ubangiji zai rushe gidajen masu girmankai, amma zai kiyaye dukiyar gwauruwa, wato mata wadda mijinta ya mutu.

26. Ubangiji yana ƙin tunanin mugaye, amma yana murna da kalmomi masu daɗi.

27. Mai ƙoƙarin cin ƙazamar riba yana jefa iyalinsa a wahala ke nan. Kada ka karɓi hanci, za ka yi tsawon rai.

28. Mutanen kirki sukan yi tunani kafin su ba da amsa. Mugaye suna da saurin ba da amsa, amma takan jawo wahala.

29. Sa'ad da mutanen kirki sukan yi addu'a, Ubangiji yakan kasa kunne, amma ba ya kulawa da mugaye.

30. Fuska mai fara'a takan sa ka yi murna, labari mai daɗi kuma yakan sa ka ji daɗi.

31. Idan ka mai da hakali sa'ad da ake tsauta maka kai mai hikima ne.

32. Idan ka ƙi koyo kana cutar kanka, idan ka karɓi tsautawa za ka zama mai hikima.

33. Tsoron Ubangiji koyarwa ce domin samun hikima. Sai ka zama mai tawali'u kafin ka sami girmamawa.

Karanta cikakken babi K. Mag 15