Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 15:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'ad da mutum yake murna yakan yi murmushi, amma sa'ad da yake baƙin ciki yakan yi nadama.

14. Mutum mai basira yana neman ilimi, amma dakikai, jahilcinsu ya wadace su.

15. Wahaltaccen mutum a ko yaushe, fama yake yi a zamansa, amma masu farin ciki suna zama da daɗin rai.

16. Gara a zauna da talauci da tsoron Ubangiji, da a sami dukiya game da wahala.

17. Gara cin mabunƙusa tare da waɗanda kake ƙauna, da ka ci abinci mai romo a inda ƙiyayya take.

18. Zafin rai yakan kawo jayayya, amma haƙuri yana kawo salama.

19. Idan kai rago ne za ka gamu da wahala a ko'ina, amma idan kai amintacce ne, ba za ka sha wahala ba.

20. Ɗa mai hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa, amma wawa yana raina mahaifiyarsa.

21. Dakikai suna murna da wautarsu, amma mai hikima zai aikata abin da yake daidai.

22. Ka nemi dukan shawarwarin da ka iya ka samu, za ka yi nasara, idan ba tare da shawara ba, za ka fāɗi.

23. Me ya fi wannan zama abin murna? Mutum ya sami maganar da take daidai a lokacin da ya dace!

24. Mutum mai hikima yakan kama hanya ya haura zuwa rai, ba ya bin hanyar da ta gangara zuwa mutuwa.

Karanta cikakken babi K. Mag 15