Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 15:13-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'ad da mutum yake murna yakan yi murmushi, amma sa'ad da yake baƙin ciki yakan yi nadama.

14. Mutum mai basira yana neman ilimi, amma dakikai, jahilcinsu ya wadace su.

15. Wahaltaccen mutum a ko yaushe, fama yake yi a zamansa, amma masu farin ciki suna zama da daɗin rai.

Karanta cikakken babi K. Mag 15