Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 14:20-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ba wanda yake son matalauci, amma attajiri yana da abokai da yawa.

21. Idan kana so ka zama mai farin ciki, sai ka nuna alheri ga matalauci. Zunubi ne ka raina kowane mutum.

22. Waɗansu za su amince da kai, su girmama ka, idan ka aikata nagarta, idan kuwa ka aikata mugunta, to, ka yi babban kuskure.

23. Idan ka yi aiki za ka sami abin masarufi, idan kuwa ka zauna kana ta surutu kawai za ka zama matalauci.

24. Mutane masu hikima za a sāka musu da wadata, amma za a san wawa ta wurin wautarsa.

25. Sa'ad da mashaidi ya faɗi gaskiya zai ceci rayuka, amma maƙaryacin mashaidi yakan ci amanar mutane sa'ad da ya faɗi ƙarairayi.

26. Tsoron Ubangiji yakan ba da tabbatarwa, da zaman lafiya ga mutum da iyalinsa.

27. Kana so ka kauce wa mutuwa? To, tsoron Ubangiji shi ne maɓuɓɓugar rai.

28. Darajar sarki ta dogara ga irin yawan mutane da ya mallaka, idan ba su, shi ba kome ba ne.

29. Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili.

30. Kwanciyar rai lafiya ce ga jiki, amma kishi yana kama da ciwon da yake cin ƙashi.

31. Wanda ya zalunci matalauci ya zargi Mahaliccinsa ke nan, amma nuna alheri ga matalauci yin sujada ne.

32. Muguntar mugun takan kawo hallakarsa, amma adalin mutum, an kiyaye shi ta wurin dattakonsa.

33. Hikima tana cikin kowane tunani na haziƙi, wawa bai san kome game da hikima ba.

34. Adalci yakan ɗaukaka al'umma, amma zunubi yakan kunyatar da al'umma.

35. Sarakuna suna jin daɗin ƙwararrun 'yan majalisarsu, amma sukan hukunta waɗanda suka ba su kunya.

Karanta cikakken babi K. Mag 14