Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 13:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Adalci yakan kiyaye marasa laifi, amma mugunta ita ce fāɗuwar masu zunubi.

7. Waɗansu mutane sukan nuna su attajirai ne, alhali kuwa ba su da kome. Waɗansu kuma sukan nuna su matalauta ne, alhali kuwa suna da dukiya.

8. Kuɗin attajiri suna iya ceton ransa, bai kyautu ba a razana matalauci.

9. Adalai suna kama da haske mai haskakawa ƙwarai, mugaye kuwa suna kamar fitilar da take mutuwa.

10. Fāriya ba ta kawo kome sai wahala. Hikima ce a nemi shawara.

11. Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, za ka rasa ta da sauri, amma wanda ya same ta da wahala, za ta yi ta ƙaruwa.

12. Idan ba bege, sai zuciya ta karai, amma muradin da ya tabbata zai cika ka da sa zuciya.

13. Idan ka ƙi shawara mai kyau wahala kake nemar wa kanka, idan ka bi ta kuwa za ka zauna lafiya.

14. Koyarwar masu hikima maɓuɓɓugar rai ce, za ta taimake ka ka kuɓuta sa'ad da ranka yake cikin hatsari.

15. Basira takan sa a girmama ka, amma mutanen da ba za a iya amincewa da su ba, a kan hanyar hallaka suke.

16. Mutum mai hankali a ko yaushe yakan yi tunani kafin ya aikata, amma wawa yakan tallata jahilcinsa.

17. Manzanni marasa aminci sukan haddasa wahala, amma waɗanda suke amintattu sukan kawo salama.

Karanta cikakken babi K. Mag 13