Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 13:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ka lura da irin abin da kake faɗa don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa.

4. Rago yakan ƙosa ya sami wani abu ainun, amma sam, ba zai samu ba. Mai mai da hankali ga aikinsa zai sami kowane abu da yake bukata.

5. Masu aminci suna ƙin ƙarairayi, amma maganganun mugun abin kunya ne da ƙasƙanci.

6. Adalci yakan kiyaye marasa laifi, amma mugunta ita ce fāɗuwar masu zunubi.

7. Waɗansu mutane sukan nuna su attajirai ne, alhali kuwa ba su da kome. Waɗansu kuma sukan nuna su matalauta ne, alhali kuwa suna da dukiya.

8. Kuɗin attajiri suna iya ceton ransa, bai kyautu ba a razana matalauci.

9. Adalai suna kama da haske mai haskakawa ƙwarai, mugaye kuwa suna kamar fitilar da take mutuwa.

Karanta cikakken babi K. Mag 13